Kuwait za ta baiwa kasashen Afrika bashi

Image caption Sarkin Kuwait, Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Sabah

Sarkin Kuwait ya yi alkawarin bada rancen tsabar kudi dala biliyan daya ga kasashen Afirka.

Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Sabah ya yi wannan alkawarin ne yayin da yake bude taron koli karo na uku tsakanin Afrika da kasashen larabawa a birnin Kuwait.

Shugabannin kasashe 34 ne suka halarci taron, da nufin karfafa zuba jari a Afrika daga kasashen yankin Larabawa.

Sarki Sabah ya ce bashin wanda ke da rangwamen ruwa zai kasance ne na tsawon shekaru biyar.

Karin bayani