Ana taron saka jari a harkar mai a Nijar

matatar mai ta Nijar
Image caption Nijar ta zama daya daga cikin kasashe masu arzikin mai bayan da aka bude matatar manta.

A Nijar an bude wani taron saka jari a harkokin man fetur da iskar gas da ma'adinai na nahiyar Afrika.

Wannan ne karo na 16 da ake shirya irin wannan taron, wanda za a yi kwana biyar.

Nijar ta karbi bakuncin taron ne a bana, tare da hadin gwiwar kungiyar CNUCED mai kula da kasuwanci da ci gaban kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya.

Nijar na fatan koyo daga irin kwarewar sauran kasashen da ke halartar taron a harkar mai da iskar gas da ma'adinai.