Jonathan ya dage gabatar da kasafin kudi

Image caption Wasu dai na ganin shugaban na tsoro ne kada a yi masa bore

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan, ya dage gabatar da kasafin kudin 2014 da zai yi ranar Talata.

A sakon da shugaban Nigeriar ya aikewa 'yan Majalisar Dokokin kasar, ya bayyana cewa ya dakatar da gabatar da kasafin kudin ne saboda a bai wa 'yan majalisar -- na dattawa da wakilai-- damar daidaita ra'ayoyinsu kan batun kayyade kudin da za a rika sayar da gangar man fetur.

Mista Jonathan ya kara da cewa da zarar majalisun sun daidaita kansu game da farashin gangar man zai je gabansu domin gabatar musu da kasafin kudin na badi.

Sai dai wasu majiyoyi sun shaidawa BBC cewa shugaba Jonathan ya ki gabatarwa 'yan majalisar kasafin kudin ne saboda rahotannin da ke cewa wasu 'yan majalisar sun sha alwashin yi masa bore saboda rashin aiwatar da kasafin kudin shekarar 2013.

Karin bayani