Dakarun Assad sun kwace birnin Qara

Image caption Shugaba Assad na ganawa da dakarunsa

Sojojin Syria sun karbe ikon birnin Qara dake iyaka da kasar Lebanon wanda ada ya kasance mashigar da 'yan tawaye ke shigar da kayayyaki zuwa sansanoninsu a yankunan dake wajen Damascus.

A yanzu gwamnatin ta kwace iko da hanyar da ta hade yankin gabar ruwan da kuma babban birnin kasar.

Sojojin sun kaddamar da farmaki ne a ranar Juma'a, lamarin da ya sanya 'yan Syrian kusan dubu goma tserewa ta kan iyakar zuwa cikin Lebanon.

Majiyoyin soji sun ce an kashe 'yan tawaye da masu yawa.

Kungiyoyi da dama na 'yan bindiga a Syria sun yi barazanar kai hari wuraren 'yan Shi'a a Lebanon domin daukar fansa bisa rawar da Hezbullah da kuma Iran ke takawa na taimakawa shugaba Assad.

Karin bayani