Yau ce ranar makewayi ta duniya

Megawayi maras inganci
Image caption Galibi a kasashe masu tasowa ake fama da matsalar magewayi maras inganci

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware dan jan hankalin jama'a kan mahimmancin makewayi.

Majalisar ta ce kimanin mutane Biliyan Biyu da rabi ne ba su da makewayin da ya dace.

Wasu sama da biliyan daya kuma suna yin bahaya a fili.

Majalisar ta ce yin bahaya a waje na kara jawo ko yada cututtuka tsakanin jama'a.