Rarrabuwa tsakanin Indonesia da Australia

Image caption Shugaban Indonesia, Yudhoyono da Firaiminista Abbott

Shugaban kasar Indonesia, Susilo Bambang Yudhoyono ya dakatar da kawancen hadin gwiwa tsakanin kasarsa da Australia ta fannin soji wanda ke da nufin magance matsalar safarar mutane.

Daukar matakin ya biyo bayan sabanin da ya shiga tsakanin kasashen ne a game da zargin leken asiri.

Rahotannin kafofin yada labarai sun ce Australia ta rika tatsar maganganun wayar tarho na shugaban Indonesia.

Gwamnatin ta Indonesia, ta bayyana bacin rai kan batun inda ta nemi bayani daga Firaministan Australia Tony Abbott.

Ministan harkokin wajen Indonesia, Dr Marty Natalegawa ya ce lamarin satar leken asiri haramun ne.

Karin bayani