Microsoft zai sayi kamfanin Nokia

Wayar Nokia da tambarin Microsoft
Image caption Cinikin zai hada da sauyi a shugabancin kamfanin na Nokia

Masu hannun jari a kamfanin wayar salula ta Nokia sun amince a sayar wa Microsoft kamfanin a kan euro miliyan dubu biyar da miliyan 400.

Za a sayar da kamfanin ne kuwa duk da cewa wasu masu hannun jarin sun ki amincewa da sayar da kamfanin na kasar Finland.

Kashi 99 da rabi cikin dari na masu hannun jari a kamfanin su 3900 ne suka amince a sayar da shi.

Cinikin zai tabbata ne bayan hukumomi sun amince kuma ana sa ran komai zai kammala zuwa farkon sabuwar shekara.

Kasuwar wayoyin kamfanin na Nokia na ja da baya yayin da ta abokan gogayya irinsu Apple da Samsung ke bunkasa.