Obama ya bukaci a yi wa Iran jinkiri

Barack Obama
Image caption Isra'ila na sukan Obama da sassauta wa Iran

Shugaban Amurka Barack Obama ya bukaci 'yan majalisar dattawan kasar da su dakata da sake kakabawa Iran sabon takunkumi, don bai wa manyan kasashen duniya damar cimma yarjejeniya ta wucin gadi a kan shirinta na nukiliya.

Kakakin fadar Amurkan ta White House, Jay Carney, ya ce idan ba a cimma wannan yarjejeniyar wucin gadi ta watanni shida ba, to Tehran za ta ci gaba da shirinta na nukiliyar.

A yau Laraba ne dai ake sa ran soma wani sabon zagaye na tattaunawa tsakanin Iran da wasu manyan kasashen duniya a birnin Geneva.

Sai dai Mr. Obama ya ce bai sani ba ko za a iya cimma yarjejeniya a wannan makon ko kuma na gaba, amma ya na ganin ko ba komai yarjejeniyar ta watanni shida za ta ba bangarorin biyu karin lokacin yin nazari kan mataki na gaba.

Karin bayani