'Amurka ba za ta nemi afuwar Afghanistan ba'

Mai bai wa Obama shawara kan tsaro Susan Rice
Image caption An ce da wasikar za kuma ta bukaci a bar sojojin Amurka su shiga gidajen 'yan Afghanistan in da bukatar hakan.

Babbar mai ba shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Susan Rice, ta ce Amurka ba za ta nemi kowace afuwa ba daga Afghanistan saboda kura-kuran da ta tafka a shekaru 12 da tayi tana yaki a kasar.

Rahotannin farko dai sun ce Amurka ta yi tayin aika wata wasika zuwa ga shugabannin kabilun Aghanistan wadda a cikinta za ta amsa cewa ta tafka kura-kurai a cikin kasar, a wani yunkuri na ceto yarjejeniyar tsaro da aka rattaba wa hannu kan makomar sojojin Amurka a Afghanistan din bayan shekarar 2014.

Da take magana ta gidan tallabijin na CNN, Jam'iar ta yi fatali da rahotannin da ke ambato wasu manyan Jami'an Afghanistan na cewar tuni har Amurka ta rubuta daftarin wasikar da za ta gabatar wajen wani taro da shugabannin kabilun Afghanistan din ranar Alhamis.

Jami'ai a birnin Kabul, sun ce Shugaba Hamid Karzai, da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, sun zanta ta wayar tarho ranar Talata inda suka warware wasu batutuwa da ke karan tsaye ga samun nasarar sabuwar yarjejeniyar tsaron.

Karin bayani