Kisan kiyashi a kasar Afrika ta Tsakiya

Wani kauye ke nan da aka sanya wa wuta a kasar
Image caption Ana ta samun hare haren ramuwar gayya tsakanin musulmi da kiristoci

Faransa ta yi gargadin cewa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na gab da fadawa masifar kisan kiyasi.

A wata hira da aka yi da ministan harkokin waje na Faransa ta talabijin Laurent Fabius ya ce rikicin kasar ya tsananta al'amura sun lalace.

Saboda haka Majalisar Dinkin Duniya na duba yuwuwar bai wa dakarun kasashen Afrika da Faransa damar shiga rikicin don tabbatar da zaman lafiya.

Tun a watan Maris kasar ta fada cikin rikici lokacin da hadakar 'yan tawaye ta hambarar da gwamnatin kasar ta baya.