Ana shirin kulla yarjejeniya akan dumamar yanayi

Image caption Kungiyoyin kare muhalli na nuna damuwa kan dumamar yanayi

Ana kan hanyar shiga rana ta karshe a wani sabon Yunkuri da ake na ganin an kulla wata yarjejeniya akan dumamar yanayi a wani babban Taro dake gudana a Kasar Poland.

Kungiyoyin kare muhalli dai sun fice daga tattaunawar a ranar Alhamis, bayan sun zargi wasu gwamnatoci da kin daukar matakan da suka dace wajen rage gurbataccen hayakin da suke fitarwa

Masu aiko da rahotanni sunce kasashe matalauta na ganin cewa dole ne Kasashe masu arziki su biya ta'adin da dumamar yanayi ya janyo a duniya, saboda a cewarsu sune ke gurbata yanayin.

Amma Kasashen da suka cigaban, sunce dole na Kasashe irinsu China da India su amince da cewa suma suna da nasu kamashon.

Karin bayani