Ana tattaunawa da Joseph Kony don ya mika wuya

Image caption Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru masu yawa da aka san inda Joseph Kony yake.

Gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta ce tana ci gaba da tattaunawa da madugun mayakan tawayen Uganda Joseph Kony da zimmar ganin ya mika wuya.

Wani mai magana da yawun gwamnatin ya shaidawa BBC cewa Mr. Kony na cikin kasar amma ya na son a ba shi tabbacin kare lafiyarsa kafin ya mika kansa.

Kotun Hukumtan Manyan Laifuka ta Duniya dai na neman shugaban na rundunar 'yan tawaye ta LRA Joseph Kony kan zarge-zargen aikata laifukan yaki.

Amurka dai ta yi tayin ladar dala miliyan uku ga wanda ya taimaka wajen kama shi.

Karin bayani