Wani jirgi ya kai hari Pakistan

shugaban 'yan Taliban da aka kashe Hakimullah Mehsud
Image caption An kai hari da jirgin maras matuki ne wata guda da aka kai hari irin wannan da ya hallaka shugaban 'yan Taliban Hakimullah Mehsud

Rahotanni daga Pakistan na cewa ana zargin jirgin yakin Amurka maras matuki ya hallaka kimanin mutane shida a wata cibiyar addinin musulunci.

An kai harin ne a yankin Khyber-Pakhtunkhwa da ke wajen kabilun Pakistan inda wani jirgin Amurkan maras matuki ya taba kai hari.

Wanna dai shi ne hari na farko da aka kai tun bayan harin da ya kashe shugaban Taliban Hakimullah Mehsud a farkon wannan watan, a na gobe za a fara tattaunawar da aka shirya yi tsakanin kungiyar masu kaifin kishin Islaman da gwamnatin Pakistan.

A jiya Laraba ne jami'an gwamnatin Pakistan suka sanar cewa Amurka ta ba da tabbacin ba za ta kara kai hari da jirgi maras matuki ba, yayin da gwamnati ke kokarin sasantawa da 'yan Taliban din.

Karin bayani