Ana koyawa mata masu yoyon fitsari sana'a

Mata masu cutar yoyon fitsari na fuskantar tsangwama daga al'uma.
Image caption Likitoci sun bayyana cewa doguwar nakuda na daya daga cikin dalilan da ke haddasawa mata yoyon fitsari, musamman idan ba'a kai su asbiti akan lokaci ba.

Sama da matan da suka gamu da cutar yoyon fitsari 150 ne a yanzu haka ke koyon sana'o'i daban daban, bayan sun warke daga cutar a wata cibiya a Kano.

Wata kungiya da ke taimaka wa masu cutar ce tare da tallafi daga asusun kula da yawan jama'a na Majalisar Dinkin Duniya ke koyawa matan da suka warke daga cutar sana'o'in.

Kungiyar ta ce a yanzu ana samun nasarar yiwa matan da suka gamu da cutar aiki har kuma su koma su ci gaba da rayuwa kamar da, wanda hakan ya rage irin kyamatar da ake nuna wa wadanda suka gamu da larurar a baya.

Sana'o'in hannun da ake koya wa matan sun hada da saka da dinki da da daukar hoto da sauransu.

Karin bayani