Samsung zai biya Apple karin tara

wayoyin Apple da Samsung
Image caption Ana sa ran kamfanin Samsung zai daukaka kara kan shari'ar

Wata kotu a Amurka ta kara yawan tarar da kamfanin Samsung zai biya na Apple da dala miliyan 290 saboda satar wasu fasahohinsa.

Fasahohin da kamfanin na Samsung ya kwaikwaya na na'urori ko wayoyin iPhone da iPad ne.

Yanzu kamfanin na Samsung na Korea zai biya Apple na Amurka tarar dala miliyan 930.

Kamfanin Apple ya ce ya kai karar ne domin kare fasaharsa, ba domin samun kudi ba.

Karin bayani