Za a binciki kamfanin man Nigeria

Image caption Shugaban majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal

Majalisar wakilan Nigeria za ta binciki kamfanin man kasar NNPC a kan zargin badakalar kasa bada cikakkun bayanai game da danyen mai na dala biliyan 13 da aka siyar a wannan shekarar.

Majalisar ta amince da hakanne, bayan wani kuduri da dan majalisa Haruna Manu ya gabatar, don kamfanin NNPC din ya bada bayanai game da cinikin mai a watanni takwas na shekara ta 2013.

A cewar dan Majalisa Haruna Manu, kamfanin NNPC ya ce ya saka dala biliyan 20 cikin asusun gwamnati a matsayin cinikin danyen mai daga watan Junairu zuwa Agusta, amma takardun da suka samu sun nuna cewar dala biliyan bakwai kawai NNPC din ya saka a asusun gwamnati.

Wani dan majalisa Samson Osagie ya ce " Kamfanin NNPC ya bar mutane cikin duhu game da cinikin mai a kasar".

Nigeria ce kasar da ta fi kowacce samar da danyen mai a nahiyar Afrika, amma ba ta iya tace man da take bukata saboda abinda ake zargi nada nasaba da cin hanci da rashawa.

Karin bayani