An saka ranar sake zabe a wasu mazabu a Anambra

Zabe
Image caption 'An sami kura kurai a zaben jahar Anambra'

Hukumar zaben Najeriya wato INEC ta sanya ranar 30 ga watan Nuwamba domin sake gudanar da zabe a wasu mazabu a jihar Anambra dake Kudu maso gabashin kasar.

Zaben gwamnan jihar Anambra dai ya janyo ce-ce ku-ce a kasar, inda wasu ke kira da a soke zaben baki- daya.

Wasu kuma cewa suke ya kamata shugaban hukumar zaben Farfesa Attahiru Jega ya yi murabus .

Shugaban hukumar zaben Farfesa Attahiru Jega ya fadawa BBC cewa an sami kura kurai a wancan zaben, wasu ma ya ce ya shafi wani ma'aikacin hukumar.

Sai dai ya ce hukumar zabe tana gudanar da bincike yanzu haka.

Jega ya kara da cewa sun gudanar da zabe a kananan hukumomi 21 a jahar Anambra amma a karamar hukuma guda daya kachal aka sami kuskure.

Karin bayani