Sabon takunkumi kan kasar Iran

Tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran a Geneva
Image caption Tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran a Geneva

Wani sanatan Amurka Harry Reid ya ce majalisar dattawan kasar za ta yi kudirin sakawa Iran karin takunkukumi a farkon wata mai zuwa.

Sanatan dan jam'iyar Democrat ya ce za a dau wannan mataki ne muddin ba a cimma daidaito a tattaunawar Geneva kan shirin nukiliyar ba.

Manyan kasashen duniya shida ne har da Amurka suka bukaci yarjejeniyar wucin gadi wacce kasar Iran din za ta dakatar da aikin inganta sinadarin Uranium, don dage mata wasu daga cikin takunkumin da manyan kasashen suka sanya mata.

Manyan kasashen duniyar dai na cikin wata tattaunawa mai sarkakiyar gaske da Iran din a Geneva.

Bayan kwanaki biyun da aka shafe ana tattaunawar, wani wakilin kasar Iran a taron kuma mukaddashin ministan harkokin kasasshen waje Abbas Araqchi ya shaida wa tashar gidan talabijin ta Iran da ke Geneva cewa zai yi wahala a cimma wata yarjejeniya.