'Yan jarida sun yi biris da umarnin Zuma

Image caption Ana zargi an gina rukunin gidajen da kudaden haram.

Jaridun Afirka ta kudu sun yi biris da umarnin shugaban firka ta kudu, Jacob Zuma, inda suka wallafa hoton wani rukunin gidajensa da ake zargi an gina da kudin cin hanci.

Wata jarida da ta wallafa hoton rukunin gidajen, ta kara da cewa '' mun wallafa idan ka isa ka sa a kama mu''.

Shugaban dai ya ce wallafa hoton ya sabawa dokokin tsaron kasar.

Hukmar da ke kare muradin 'yan kasar tana gudanar da bayan da aka bayyana cewa an yi wa rukunin gidajen kwaskwarima kan kusan dala miliyan 20 .

Karin bayani