Angola: 'Yan adawa sun yi zanga-zanga

Image caption Dos Santos, shugaban kasar Angola

A Angola 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma yin harbi a iska domin tarwatsa magoya bayan 'yan adawa dake zanga-zangar nuna rashin amincewa da batan dabo da wasu masu fafutuka biyu suka yi.

An dai yi zanga-zangar ce a Luanda, babban birnin kasar, kuma jam'iyyar adawa ta UNITA da ta yaki gwamnatin MPLA tsawon shekaru ashirin da bakwai ce ta shirya shi.

Jam'iyyar adawa ta UNITA ta ce, an kama magoya bayanta da dama.

A farkon wannan watan ne da shugaban kasar Angolan ya sallami babban jami'in leken asirin kasar saboda zargin cewa, akwai hannun jami'an tsaro a batan wasu masu fafutuka biyu.