Masar ta kori jakadan Turkiyya a kasarta

Image caption Shugaban rikon kwayar Masar, Adly Mansoor

Hukumomin Masar sun umarci jakadan kasar Turkiyya ya fice daga kasar, kuma suka ce, sun rage dankon huldar diplomasiyya tsakanin ksashen biyu.

Masar ta dauki wannan mataki ne domin nuna rashin amincewa da irin goyon bayan da Turkiyya take baiwa hambararren shugaban Masar, Muhammad Morsi:

Wakilin BBC yace: Korar jakadan Turkiyya da gwamnatin Masar tayi ya kara dagula dangantar da tayi tsami tsakanin kasashen biyu tun bayan da soja suka hambare gwamnatin Muhammad Morsi, mai ra'ayin Islama.

Karin bayani