John Kerry zai halarci taro kan Iran a Geneva

Taron Geneva kan nukiliyar kasar Iran
Image caption Taron Geneva kan nukiliyar kasar Iran

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zasu halarci taron taron kasa da kasa kan shirin nukiliyar kasar Iran da ke gudana a Geneva.

Wannan mataki dai na zuwa ne yayin da ake shaci fadin cewa mai yiwuwa a rufe batun yarjejeniyar.

Masu tattaunawar daga kasar Iran da manyan kasashen duniya 6 ciki har da Amurka sun shafe kwanaki uku suna kokarin shawo kan matsalar banbance-banbancen da ke tsakaninsu.

Ofsishin huddar jakadancin Amurka a Iran ya bada sanarwar cewa, Mr Kerry zai halarci taron ne don ci gaba da taimakawa wajen kawo karshen matsalar banbance-banbancen dake tsakani don cimma yarjejeniyar.

Manyan kasashen duniyar 6 dai na yunkurin cimma yarjejeniyar watanni 6 ta wucin gadi da kasar Iran- mataki na farko da zai sa kasar ta sassauta shirinta na makaman nuclear, a madadin yi mata rangwame kan takunkumin kasa da kasa da aka kakaba mata.