Kokarin cimma matsaya kan shirin nukiliyar Iran

Taro kan shirin nukiliyar Iran
Image caption Taro kan shirin nukiliyar Iran

Ministocin hulda kasashen wajen wasu kasashe da suka shiga tattaunawa akan shirin nukiliyar Iran dake taro a birnin Geneva sun ce, har yanzu akwai wasu batutuwan da sai an warware su ne za'a kai ga cimma wata matsaya.

Yayin da ya isa wurin taron sakataren hulda da kasashen wajen Birtaniya, William Hague yace, akwai dan bambanci akan wasu batutuwa tsakanin manyan kasashen nan shida da kuma Iran:

Wakilin BBC yace: Jami'an diplomasiyya sun ce, suna fatan cimma wata yarjejeniya ta wucin gadi da Iran, amma kuma babu tabbas ko za'a cimma takamaimiyar matsaya akan batun..

Ministan hulda da kasashen wajen Jamus Guido Westerwelle yace, duk da irin bambace-bambancen dake akwai tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, akwai fatan za'a cimma wata matsaya

Karin bayani