Zimbabwe za ta soma kama 'Yan kasuwar Najeriya

Shugaba Robert Mugabe
Image caption 'Yan zimbabwe na ganin baki suna hana su kasuwanci

Daga ranar daya ga watan janairun shekara mai zuwa , za'a fara kama 'yan kasashen waje masu shaguna a kasar Zimbabwe.

Hakan ya biyo bayan damuwar da gwamnatin Zimababwe ta nuna akan yawan 'yan kasuwar Najeriya da kuma China dake tururuwa zuwa kasar.

Wani babban jam'i a ma'aikatar karfafa bakar fata a Zimbabwen ya ce 'yan Kasar ne kadai ke da ikon kafa shaguna.

Wasu 'yan Zimbabwen dai na ganin cewa kamata ya yi bakaken fata su hada kansu ba tare da suna musgunawa juna ba.

Ana dai sukar masu shaguna da suka fito daga Kasashen waje da mamaye damar da 'yan Zimbabwe ke da shi na gudanar da harkokin kasuwanci a cikin Kasar su.

Karin bayani