An kashe mutane sha-biyu a Borno

'Yan Boko Haram
Image caption 'Yan kungiyar Boko Haram

'Yan sandan Nijeriya sun ce, an kashe akalla mutane goma sha-biyu tare da kona gidaje da dama a wani kauye dake jihar Borno.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce, wasu 'yan bindiga ne dake tafe a jerin gwanon motoci da babura suka aukawa kauyen na Sandiya a ranar Alhamis.

Shaidun sun ce, wadanda suka kai harin 'yan kungiyar Boko Haram ne dake zargin mazauna kauyen da hada baki da jami'an tsaro.

Saboda tsunke layukan salula da aka yi a yankin sai yanzu labarin ya bulla, mutanen kuma da suka samu tsira daga harin, sai da suka yi tafiyar kimanin kilomita dari kafin su isa Maiduguri, baban birnin jihar Bornon.

Karin bayani