Dokar takaita 'yancin zanga zanga a Masar

Adly Mansour shugaban gwamnatin wucin gadin Masar
Image caption Wasu na ganin an yi dokar ne da nufin muzguna wa magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi

Shugaban wucin gadi na kasar Masar, ya sanya hannu akan wata doka da za ta takaita hakkin mutane na yin zanga-zanga.

Kafofin yada labaran gwamnati sun ce, Adli Mansour ya sanya hannu akan dokar wacce kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka ce, za ta danne hakkin jama'a na yin zanga-zangar lumana.

Sabuwar dokar dai za ta bukaci duk masu shirin yin zanga-zanga su nemi izinin 'yan sanda.

Shugaban ya sanya hannu akan wannan doka ne kusan makonni biyu bayan dage dokar ta baci da kuma ta hana fita da aka sa a duk fadin kasar.

Karin bayani