Nukiliya: An cimma yarjejeniya da Iran

Tattaunawar yarjejeniya kan Iran a Geneva
Image caption Tattaunawar yarjejeniya kan Iran a Geneva

Bayan wata tattaunawa a Geneva, Iran da manyan kasashen duniya shida sun cimma yarjejeniya kan shirinta na nukiliya mai cike da takaddama.

Nan gaba kadan ne ake sa ran shugaban Amurka Barack Obama zai yi jawabi game da yarjejeniyar.

Dama dai Amurka ta yi alkawarin sassauta takunkumin tattalin arziki ga Iraniyawa muddin aka cimma yarjejeniyar. A nata bangaren Iran ta nuna karara cewa ba za ta amince da yarjejeniyar da zata haramta mata ci gaba da bunkasa makamashin Uranium ba.

Jim kadan bayan kammala yarjejeniyar ne shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya bayyana a shafin sada zumunta na twitter cewa ya yi na'am da yarjejeniyar da aka cimma a Geneva.

Mr Rouhanin ya kuma ce wannan muhimmiyar tattaunawa ta bude wani sabon babi na kawo ci gaba.