Ranar yaki da cin zarafin mata

Wasu mata a jamhuriyar Nijar sun koka
Bayanan hoto,

Wasu mata a jamhuriyar Nijar sun koka

Wasu mata a jamhuriyar Nijar sun koka ga yadda ake ci musu zarafi yayin da ake bikin ranar yaki da cin zarafin mata ta duniya.

Matan sun koka musamman kan irin wahalhalun da suke sha a gidajensu na aure.

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar 25 ga watan Nuwamban kowace shekara ne domin yin nazari tare da fadakar da jama'a illolin da ke tattare da cin zarafin mata.

Wani kiyasi na Majalisar ya nuna cewa kimanin kashi saba'in cikin dari na yawan matan duniya sun taba fuskantar wani nau'in cin zarafi a rayuwarsu.