An kashe dakaru 900 a rikicin Congo

Image caption Dakarun 'yan tawaye

Sojojin Congo sun ce rikicin da aka yi tsakaninsu da 'yan tawayen M23 ya janyo rasuwar dakaru fiye da 900 tun daga watan Mayu.

Kakakin sojin Janar Jean-Lucien Bahuma, ya ce an kashe sojoji fiye da 200 sannan kuma an kashe 'yan tawaye fiye da 700 a gumurzun da aka yi a gabashin Jamhuriyar Demokradiyar Congo.

A farkon wannan watan ne, dakarun gwamnatin Congo masu samun goyon bayan Majalisar dinkin duniya suka samu galaba a kan 'yan tawayen M23.

Kawo yanzu gwamnati da 'yan tawayen sun kasa cimma matsaya game da yarjejeniyar zaman lafiya.

Karin bayani