Shagulgula kan yarjejeniyar nukiliyar Iran

Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif
Image caption Ministan wajen Iran Mohammed Javad Zarif ya ce kasar za ta aiwatar da sharuddan yarjejeniyar

Jama'a da dama ne a Iran suka yi shugulgula lokacin da masu tattaunawa suka komo daga Geneva, bayan kulla yarjejeniyar nukiliya da kasashen duniya shida.

A bisa yarjejeniyar, Iran, ta amince ta sassauta shirinta na bunkasa makamashin Uranium har na tsawon watanni shida, yayin da aka sassauta mata wasu daga cikin takunkumin da manayan kasashen duniya suka sa mata.

Shafukan farko na Jaridun kasar da dama sun buga labaran da ke dauke da yadda jama'a ke yin marhabun da yarjejeniyar, yayin da shafukan sada zumunta na intanet ke cike da ra'ayoyi daban daban game da batun.