''Dole a daina kai hari kan gidajen fararen hulla''

Image caption Majalisar ta Loya jirga dai ta bukaci Karzai da ya sa hannu kan yarjejeniyar nan take, amma shi yana son jinkirta yin hakan har zuwa bayan zaben kasar.

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai ya bukaci sojojin Amurka da su dakatar da kai kowane irin farmaki a kan gidajen fararen hula, kafin ya amince da karin wa'adin zaman Sojojin a kasarsa.

Ya yi wannan jawabi ne yayin wata tattaunawa da mai ba shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Susan Rice.

Ya ce kuma dole ne a saki 'yan Afghanistan da ake tsare da su a sansanin ihunka-banza na Guantanamo Bay.

A ranar lahadin da ta gabata ne majalisar hugabannin al'umomin kasar da ake kira da Loya Jirga suka amince da karin wa'adin zaman sojojin Amurkar galibi masu ba da horo a Afghanistan din tare da kira ga shugaba Hamid Karzai ya rattaba hannu kan yarjejeniyar ba tare da bata lokaci.

Karin bayani