An kashe mutane tara a Libya

Tashin hankali a Benghazi
Image caption Fada tsakanin dakarun gwamnati da 'yan gawagwarmaya masu kishin Islama ya zama jiki a Benghazi

An yi mummunan dauki ba dadi tsakanin dakarun gwamnati da kuma mayaka masu tsattsauran kishin Islama a Beghazi da ke gabashin Libya.

An kashe akalla mutane tara wasu hamsin kuma sun samu raunuka a fadan da aka fafata tsawon sa'oi.

Jami'an tsaro sun ce fadan ya barke ne lokacin da aka kai hari kan wani mutum farar hula a wani wurin binciken ababan hawa na masu kishin Islaman, Ansar al-Sharia.

Ana ganin fadan a matsayin sa-in-sa mafi muni tsakanin dakarun gwamnati da kungiyar 'yan gwagwarmayar.

Ana dora alhakin kisan alkalai da jami'an tsaro da dama akan wannan rashin jituwa.