Matasa masu dauke da HIV sun karu

gwajin kwayar cutar hiv
Image caption gwajin kwayar cutar hiv

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan matasa dake kamuwa da kwayar cutar HIV wadda kan kai ga cutar AIDS mai karya garkuwar jiki sun karu da kimanin kashi daya cikin kashi ukku a shekaru goma da suka wuce.

Kungiyar lafiyar ta duniya ta ce matasa fiye da miliyan biyu ne wadanda shekarunsu na haihuwa suka kama daga goma zuwa sha tara a yanzu haka suke dauke da kwayar cutar.

Kungiyar ta dora alhakin karuwar cutar akan rashin nagartaccen tsari na taimakawa rukunin matasan.

A nahiyar Afirka kudu da hamadar sahara galibin wadanda suka kamu da cutar 'yan mata ne wadanda basa daukar matakan kariya yayin saduwa.

A nahiyar Asia kuma an gano cutar ta fi addabar matasa wadanda ke tu'ammali da miyagun kwayoyi

Karin bayani