CAR: Faransa za ta tura karin sojoji

Image caption Dakarun Faransa

Jami'an agajin gaggawa na majalisar dinkin duniya dake jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na yin kira da a gaggauta kawo karshen tashin hankalin dake kara kamari a kasar.

Wani mai magana da yawun asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya ya ce kungiyoyin 'yan banga da kuma na 'yan tawaye sun dukufa wajen wasashe dukiyoyin jama'a ba tare da la'akari da fararen hula ba.

Tun farko dai Faransa ta ce za ta kara tura daruruwan sojoji zuwa Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, domin kare kasar daga wargajewa.

A cewar jami'an majalisar dinkin duniya, sannu a hankali jamhuriyar Afirka ta tsakiyar ta na fadawa cikin halin rudu, yayin da gwamnatin wucin gadin kasar ta kasa kawar da kungiyoyin sa-kai da kuma 'yan tawaye.

Wasu na gargadin cewa mai yiwuwa a shiga kisan kare dangi a kasar.

Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Jan Elliasson ya yi kira ga kwamitin tsaro ya dauki mataki kan halin da fafaren hula ke ciki a jamhuriyar Afirka ta tsakiya na kunci fiye da kima.

Mr Elliasson ya ce ana samu yawaitar fyade da azabtarwa da kisan mummuke da kuma rikicin addini tsakanin Musulmi da Kirista.

Karin bayani