Kompany ya koma horo tare da City

Image caption Vincent Kompany

Kyaftin din Manchester City, Vincent Kompany ya koma horo da tawagar 'yan kwallon kungiyar bayan ya yi jinyar makwanni shida.

Dan kwallon baya na Belgium, ya ji rauni ne a wasansu da Everton a ranar 5 ga watan Okotoba, amma a ranar Talata ya koma horo a filin Etiham.

Babu tabbas a kan ko zai taka leda a wasansu da Viktoria Plzen na gasar zakarun Turai a ranar Laraba.

Sai dai kuma har yanzu David Silva, Stevan Jovetic da kuma Jack Rodwell zasu ci gaba da jinya.

Karin bayani