Shin PDP ta zama jam'iyyar adawa ne?

Image caption Masana harkokin siyasa sun ce hakan zai yi tasiri a zaben 2015

Jama'iyar PDP ta bayyana cewar ba ta damu matakin hadewa da jama'iyar adawa ta APC da 'yan sabuwar Jama'iyar PDP, wadanda suka balle daga cikinta, suka dauka ba.

Ta bukaci dukanin yayanta a Najeriya su kasance masu mayar da hankali da kuma sasantawa, da yake yanzu masu neman janye mata hankali sun fice daga cikinta.

Jama'iyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwar da ta bayar a Abuja.

Tana mai cewar ita jama'iya ce mai la'akari da yancin dukanin yan Najeriya na yin zabin abinda ya fi masu.

Jama'iyar ta PDP ta ce, daga wannan sauyin sheka yan sabuwar Jama'iyar PDP sun bayyana aniyarsu kururu, wadda galibin yan Najeriya suka hanga, na barin babbar jama'iya, suka rungumi wani gungun masu nunin banbancin kabilanci da addini wadanda babbar aniyarsu iya ce ta haddasa tashin hankali a Najeriya.

Jama'iyar ta ce tun daga hukuncin kotu ya kasance babu wani bangare a jama'iyar.

Haka nan kuma jama'iyar ta yaba wa shawarar wasu daga cikin gwamnonin masu korafi da suka tsame kansu daga matakin wasu takwarorinsu.

Matakin da gwamnoni shida na sabuwar PDP suka dauka na hadewa da APC ya bar jam'iyyar PDP da gwamnoni 17 cikin 36.

Don haka yanzu gwamnonin jam'iyyar APC sun koma 17 daga 11 da suke dasu lokacin da jam'iyyar ACN da ta CPC da ANPP da wani bangaren APGA duka hade a farkon wannan shekarar.

Masana harkokin siyasa dai sun ce hakan na nufin jam'iyyar ta PDP ta kama hanyar komawa jam'iyyar adawa a kasar.

Haka kuma Majalisar Dokokin kasar, wacce jam'iyyar PDP ke da rinjaye, ta kama hanyar komawa hannun 'yan adawa.

Saboda a halin yanzu idan har 'yan sabuwar PDP suka hade da gwamnonin jihohinsu, tabbas za su iya kwace ragamar shugabancin majalissun biyu saboda yawansu.

Kazalika, a cewarsu hakan zai yi tasiri sosai a kan zaben da za a gudanar a shekarar 2015.

'Baraka a APC'

Gwamnan jihar Niger da ke Nigeria, Mu'azu Babangida Aliyu, ya musanta cewa yana cikin gwamnonin sabuwar PDPn da suka hade da jami'iyyar APC.

Don haka a cewar gwamnan ''ina nan a cikin jam'iyyar PDP''.

Kakakin gwamnan, Danladi Ndayebo, ya ce sun yi matukar kaduwa da jin labarin cewa gwamnonin sabuwar PDP sun hade da jam'iyyar APC ganin cewa ba a daddale kan batun ba.

Ndayebo ya kara da cewa gwamnan na Niger ba ya wajen taron da 'yan sabuwar PDP suka hade da APC.

Karin bayani