An maido wa Nigeria dala miliyan 700 na Abacha

Image caption Margayi Janar Sani Abacha

Jakadan kasar Switzerland a Nigeria, Dr Hans-Rudolf Hodel ya ce an maido wa Nigeria da dala miliyan 700 na dukiyar tsohon Shugaban mulkin sojin kasar, Janar Sani Abacha.

A cewarsa, gwamnatin Switzerland da ta Nigeria, sun amince da bukatar babban bankin duniya na sake nazari a kan yadda za a saka wadanan kudaden don yin ayyukan ci gaban kasa.

Hodel ya ce "A kan batun Sani Abacha, Switzerland ta maido wa Nigeria dukiyarsa dala miliyan 700."

Jakadan ya ce Switzerland za ta tallafawa wata kungiya mai zaman kanta a Nigeria don ta sa'ido wajen gano yadda za a kashe kudaden da aka maidowa kasar.

Kan batun dan Abacha, Abba, Hadel ya ce har yanzu ana ci gaba da shari'arsa a Geneva.

Karin bayani