An kori Berlusconi daga Majalisar dattawa

Silvio Berlusconi
Image caption Silvio Berlusconi

Majalisar dattawan Italiya ta kada kuri'ar korar tsohon Pirayim Ministan kasar, Silvio Berlusconi daga majalisa -- nan take.

An hana wa Mr Berlusconi rike dukanin wani mukamin gwamnati saboda kotu ta same shi da aikata babban laifi na zambar biyan haraji.

Haka nan ma kotun ta same shi da wani laifin, amma ana jiran sakamakon daukaka karar da yayi -- ta yin lalata da karuwar da shekarunta basu kai ba.

Tuni dai Mr Berlusconi mai shekaru 77, wanda kuma ya kasance Firaminista har sau 3 -- ya shaidawa wani taron magoya bayansa a birnin Roma cewar ba zai bar fagen siyasa ba.

Karin bayani