Jiragen yakin Amurka sun keta 'hurumin' China

Image caption Da ma Amurka wadda ke da soja 70,000 a yankin ta ce ba za ta mutunta hurumin na China ba.

Wasu jiragen saman yaki na Amurka biyu sun ratsa ta sararin samaniyar yankin tekun gabashin China, ta cikin inda China ta saka a hurumin tsaronta na sararin samaniya ba tare da sanar da ita ba.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya ce jiragen samfurin US B-52 Bombers wadanda ba sa dauke da makamai sun tashi ne daga Guam ranar Litinin a wani bangare na wani atisayen da suke yi a yankin.

Kanar Steven Warren ya ce babu wata sanarwa da aka bai wa hukumomin China kafin shigar jiragen yankin, kuma jiragen sun shiga sun fito lafiya lau bayan sun kwashe kusan awa daya a cikin sararin da Chinan ta yi gaban kanta wajen saka shi cikin hurumin tsaronta na sararin samaniya.

A makon jiya ne dai China ta sanar da fadada huruminta na sararin samaniya saboda jayayyar mallakar wani zirin tsibirai da take yi da Japan a Tekun ta Gabashin China.

Karin bayani