Firaministan Latvia ya yi murabus

Image caption Firaministan Latvia, Valdis Dombrovskis

Firaministan Latvia, Valdis Dombrovskis ya yi murabus, a sakamakon rugujewar wani gini ranar Alhamis da ta wuce, inda mutane akalla hamsin da hudu suka mutu.

Mr Dombrovskis ya ce , a siyance zai dauki alhakin wannan abin takaici da ya faru, inda rufin wani babban kanti ya rufta, a babban birnin kasar wato Riga.

'Yan sanda sun fara gudanar da bincike, domin gano ko an karya ka'idojin gine-gine; don kuwa ana gina wani lambu ne a kan rufin wannan katafaren kanti, lokacin da lamarin ya auku.