'Yan cirani sun nutse a teku

Wasu mutane 'yan kasar Haiti
Image caption Yawancin wadanda suke tafiya cirani daga Haiti na neman dari da kwabo ne saboda tsananin talaucin ad suke ciki.

Jami'an Amurka masu gadin gabar tekun kasar sun ce kusan 'yan Haiti talatin ne suka nutse a cikin teku, a lokacin da kwale-kwalen da suke ciki makare da mutane ya nutse a kudu maso gabashin tsuburin Staniel Cay da ke Bahamas a daren Litinin din da ta gabata.

Wani daga cikin masu tsaro tekun ya shaida wa BBC yadda sukai aikin ceton mutanen ta hanyar kokarin isa wurin tare da jefa musu ababen da ke hana mutane nutsewa a ruwa da abinci da ruwan sha da sauran abubuwan bukata, sannan suka yi amfani da jirgin ruwa suka kwashe su.

Masu aikin ceto dai sun tserar da mutane dari da goma ,su na kuma ci gaba da laluben tekun don gano wadansu mutanen.

Karin bayani