Kasafin kudi ya sami karbuwa a Nijar

Tutar Nijar
Image caption Tutar Nijar

Majalisar dokokin Nijar ta amince da kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2014.

Kasafin kudin, wanda ya tashi biliyan dubu daya da 867 na CFA, zai bada karfi ne ga yin manya manyan ayyuka a cikin kasa.

Sai dai wasu 'yan adawa a kasar na kukan cewa ba a yi la'akari da wasu shawarwarin da suka bayar ba.

A cewarsu, kudaden da aka ware don habaka ilimi, da gyaran hanyoyi, da kuma sayen kayayakin abinci saboda rashin kyaun damana, ba su wadatar ba.

Nijar din ce za ta samar da kashi 62 cikin 100 na kasafin kudin, saura kashi 38 cikin 100 ta na sa ran samun su ne daga kasashen waje.