An kama Janar Amadou Sanogo a Mali

Janar Amadou Sanogo
Image caption Janar Amadou Sanogo

An kama babban hafsan sojan nan da ya jagoranci juyin mulki bara a Mali, Janar Amadou Sanogo.

An tuhume shi da laifin laifin aikata kisan kai da yin garkuwa da mutane.

Wasu sojoji ne aka tura da muggan makamai suka je gidan Janar Sanogo domin kai shi kotu.

Kotun ta bada umurnin a ci gaba da tsare shi.

Juyin mulkin da Janar Sanogo ya jagoranta ne ya tsunduma kasar ta Mali cikin rudu, ciki har da mamayar da masu kishin Islama su ka yiwa yankin arewacin kasar.

Ana kuma zargin sojoji da azabtar da mutane da kuma kashe su.

Wata wakiliyar BBC a Malin ta ce, mutane dayawa sun ji dadin kama Janar Amadou Sanogo.

A ganinsu wata alama ce da ke nuna cewa, sabuwar gwamnatin da aka zaba ba za ta yi wa sojoji sako-sako ba.