'Yan APC sun yi zanga-zanga kan zaben Anambra

Image caption Shugabanni APC a zanga-zangar lumana

Tsohon Shugaban Nigeria, Janar Muhammadu Buhari da tsohon gwamnan Lagos, Bola Ahmed Tinubu na daga cikin kusoshin jam'iyyar adawa ta APC da suka gudanar da zanga-zanga a Abuja zuwa shalkwatar hukumar zaben kasar wato INEC.

'Yan jam'iyyar APC din na zanga-zangar ce don neman a soke zaben gwamnan da aka yi a jihar Anambra, zaben da INEC din ta ce babu wanda ya samu nasara.

Ita dai INEC ta ce za ta gudanar da sabon zabe a wasu kananan hukumomin Anambra, a yayinda APC ke bukatar a sake sabon zabe.

Zaben gwamna a jihar ta Anambra ya bar baya da kura, sakamakon matsaloli da aka fuskanta wajen rashin isar kayayyakin zabe a wasu runfunan zabe sannan kuma ga zargi an yi amfani da jami'an INEC wajen yin aringizon kuri'u.

Sakamakon da INEC ta fitar game da zaben ya nuna cewar dan takarar jam'iyyar APGA mai mulkin jihar ne kan gaba.

Karin bayani