Gwamnati ta baiwa ASUU wa'adin kwanaki 7

Image caption Malaman jami'ar Bayero ta Kano a lokacin zanga-zanga

Gwamnatin Nigeria ta baiwa 'yan kungiyar malaman jami'o'i-ASUU wa'adin kwanaki bakwai su koma aiki ko kuma su dauki kansu a matsayin wadanda aka kora.

Ministan Ilimi, Nyesom Wike ya umurci shugabannin jami'o'i su bude jami'o'in a ranar hudu ga watan Disamba.

A cewarsa, duk malamin da bai koma bakin aiki ba, ya dauki kansa tamkar korarre.

Kungiyar ASUU ta shafe fiye da watanni biyar tana yajin aiki bisa abin da ta kira kin cika alkawarin da gwamnatin Tarraya ta kulla da ita a shekara ta 2009.

Karin bayani