Boko Haram : Kotu ta hana belin malami

Dr Muhammad Nazeef Yunus
Image caption Lauyoyinsa sun ce za su kaluabalanci umarnin da daya kotun ta bayar na ci gaba da tsare shi.

Wata kotu a Abuja ta ki ba da belin malamin nan na jami'ar jihar Kogi Dr Muhammad Nazeef Yunus da aka kama a Jos da alaka da kungiyar Boko Haram.

Malamin wanda kuma darekta ne a makarantar Islamiyya ta Al Bayan da ke Jos, hukumar tsaro ta farin kaya ta kasa SSS, ta kama shi bisa zargin cewa shi ke nemawa kungiyar Jama'atu Ahlissunnah Lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram mabiya.

Kotun ta ce ta hana belin ne domin baiwa hukumar damar ci gaba da bincike a kan malamin kamar yadda wata kotu ta daban ta ba da umarni.

Kafin shigar da kara gaban wannan kotun hukumar tsaron ta tsare malamin ba tare da iyalansa ko 'yan uwansa na samun sukunin ganinsa ba ballantana su san halin da yake ciki.

Kotun ta umarci hukumar ta SSS ta bari wasu daga cikin iyalai da 'yan uwansa suna ziyartar sa sannan kuma a bashi dama yana ganin likita kan rashin lafiyarsa.

Karin bayani