Kotun Masar ta daure mata 21 kan zanga-zanga

Image caption Daya daga cikin masu kare hakkin bil adama a kasar ya bayyana hukuncin a zaman 'hauka'.

Wata Kotu a kasar Masar ta yanke wa tarin wasu mata masu zanga-zanga su 21- ciki har da 'yan mata 7, daurin shekaru 11 a kurkuku.

Matan dai sun shiga cikin wata zanga-zanga ne da aka yi a watan jiya a birnin Askandariya domin nuna goyon baya ga hambararren shugaba Mohammed Morsi.

Iyayen daya daga cikinsu sun ce 'yarsu mai shekaru 15 ta bi ta wurin ne kawai kan hanyarta ta zuwa makaranta.

Kotun ta same su da laifin yin zagon-kasa da kuma amfani da karfi; sai dai masu rajin kare hakkin dan adam sun yi Allah-wadai da hukuncin.

Karin bayani