Nukiliya: Iran ta gayyaci hukumar IAEA

Image caption Daya daga cikin wuraren da ake zargin Iran na kokarin samar da nukiliya

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya -IAEA ta ce Iran ta gayyace ta, takai ziyara a wata muhimmiyar cibiyar dake da alaka da makamashin nukiliya, a Arak a cikin wata mai shigowa.

An yi amannar cewar cibiyar za ta iya samar da ma'adinin Plutonium a lokacin da aka kammala ta.

Ziyarar ta biyo bayan wata yarjejeniyar nukiliya ce da aka sanya wa hannu a Geneva a ranar lahadi, tsakanin Iran da manyan kasashe 6 na duniya.

Hukumar nukiliyar ta IAEA ta ce tana duba hanyar aiwatar da yarjejeniyar wadda ta nemi hana aikin nukiliyar Iran domin samun saukin takunkumin kasashen duniya.

Karin bayani