Mabarata sun yi Allah-wadai da hana bara a kano

Gwanman Jihar Kano Dr. Rabi'u Musa
Image caption A lokutta da yawa dai akan gano mabaratan da suka tara dimbin dukiya daga baran amma suke ci gaba da yinsa.

Nakasassu a jihar Kano ta arewacin Najeriya sun yi fatali da matakin da majalisar dokokin jihar ta dauka na kafa dokar hana bara a jihar, a zaman wani mataki na kuntata musu.

A cikin wannan makon ne majalisar ta amince da dokar ta hana bara wacce bangaren zartarwa ya aika mata.

''Mun ga kowane mutum a Kano gwamnati ta tanadar masa abin da zai yi; amma ban da mu. Mu kawai sai doka aka yi mana za a kama mu a daure,'' inji Aminu Ahmad Tudun Wada, Sakataren kungiyar Nakasassu ta Kanon.

Sai dai majalisar ta ce ta kafa dokar ne da nufin raba al'umma da barace barace marassa dalili.

Karin bayani