Kotun ICC ta sauya wasu dokokinta

Shugaba Uhuru Kenyatta
Image caption ICC ta ce Uhuru Kenyatta zai iya bayyana ta hanyar sakon bidiyo

Kasashe wakilan kotun duniya mai hukunta miyagun laifufuka ta ICC sun bayyana shawarar sauya dokoki domin bayar da dama ga wadanda ake kara su bayyana ta hanyar sakon bidiyo.

Sauyin zai kuma bar wadanda ake zargi masu rike da manyan mukamai su tsallake wasu lokuta na zaman shari'ar da ake masu.

Sauye- sauyen za su iya shafar shugaban Kenya Uhuru Kenyatta wanda ke shirin gurfana a gaban kotun a cikin watan Fabrairu.

Wata babbar Jami'ar kotun , Tiina Intelmann, ta shaidawa BBC cewa kotun ta amince cewa shugaban kasa na da nauyin tafiyar da mulkin kasarsa a kansa.

Karin bayani